Littafin Magana Jarice Na Biyu, Dunqule a Matsayin Application Don Sauqin Karatu
Littafin magana Jarice littafine wanda Abubakar Imam O.B.E C.O.N, L.L.D (Hon.) N.N.M.C ya Rubuta: An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa’an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya Yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar a Katsina a shekarar 1932.
Ya Rubuta Littatafai Da dama yayin rayuwarka, wadanda suka hada dashi wannan Littafi Na Magana Jarice, Ruwan Bagaja, Da Sauransu.
Magana Jarice Littafine mai dadin karatu domin ya qunshi labarai masu qayatarwa da kuma nishadantarwa daki-daki. Wajen qir-qirar application din nan, munyi iya bakin qoqari wajen ganin cewa rubutun ya zama da girma domin dadin karatu.
Wannan shine Littafi Na biyu cikin Jerukan Littafan Na Magana Jarice guda Uku, Kuma wannan littafi Offline ne, wato baya buqatar amfani da Mobile data wajen bude shi.
Dan haka ayi karatu lafiya: Ku sauraremu nan gaba akwai wasu littatafan suna zuwa da izinin Allah.
Domin bayar da shawara ta yadda zamu inganta applications dinmu za'a iya neman ta e-mail address din mu dake qasa. Mun gode.